Budurwa ta kashe kanta saboda kaɗaici a kasar Ingila

Budurwa ta kashe kanta saboda kaɗaici a kasar Ingila

Zaman kadaici yayi sanadiyyar mutuwar wata budurwa yar shekaru 28 mai suna Sharon Bukokhe yar asalin kasar Kenya dake zaune a Ingila.

Budurwa ta kashe kanta saboda kaɗaici a kasar Ingila
Sharon

Marigayiya Sharon ta kasance manaja ce a wani kungiyar sa kai, inda suke kulawa da mata tare da shawartan su game da sha’anin kayyade haihuwa.

KU KARANTA:Mu ba barayi bane - Sanatoci sun yi kaca-kaca da Buhari

Rahotanni sun bayyana cewar Sharon tana matukar kewar yan uwanta da mijinta wadanda suke nesa da ita, sakamakon danginta suna zama a kasar Canada da Amurka, yayin da mijinta ke karatu a kasar Afirka ta kudu.

Budurwa ta kashe kanta saboda kaɗaici a kasar Ingila
Sharon

Dama dai likitoci sun gano cewar Sharon tana fama da tsananin damuwa a dalilin halin kadaicin da take cki, hakan shi ya kai tag a daukan shawarar halaka kanta. Rahotanni sun shaida cewar sai da Sharon tayi kwalliya ta caba ado kafin daga bisani ta hallaka kanta.

Zaku iya samun labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel