Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga wasu hotunan auran Zahra

Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga wasu hotunan auran Zahra

- Iyalan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun ki cewa komai kan hotunan Zahra da Mohammed Indimi dake tashe

- Sunyi ikirarin cewa hotunan ba wai ainahin hotunan auren da yar su ta dauka bane

- Da suka ki amincewa da hotunan, wakilan ahlin gidan sunyi alkawarin cewa zasu saki hotunan da aka dauka don auran nan ba da jimawa ba

Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga wasu hotunan auran Zahra
Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga hotunan auran Zahra

Iyalan gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari sun ki amincewa da hotunan da ke tashe a matsayin hotunan auran Zahra da Muhammed Indimi.

Iyalan sun bayyana hakan a wani sanarwada aka saki daga Adebisi Olumide-Ajayi; maiba matar shugaban kasa shawara. Iyalan gidan sunyi ikirarin cewa hotunan na jabu ne da kuma kunyatawa a garesu.

KARANTA KUMA: Labari mai dadi: Jihar Lagas ta rarraba shinkafa mai sauki

Olumide-Ajayi ta bayyana cewa iyalan gidan shugaban kasa na son auran ya kasance na sirri kuma al’amarin yan uwa.

Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga wasu hotunan auran Zahra
Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga wasu hotunan auran Zahra

Da take Magana kan hoton gaskiya, tayi alkawarin cewa zasu saki sahihan hotuna a lokacin da ya dace.

Sanarwan ya kasance, “yazo ga iyalan buhari, cewa wasu hotuna na yawo a shafuka zumunta da kafofin watsa labarai tare da ikirarin cewa hotunan auran Zahra Buhari da Mohammed Indimi ne.

“Bayan cewa wannan hotunan ba gaskiya bane, sun kasance kunyatawa ga ma’auratan.

“Ma’auratan na so nuna cewa kamar yadda suke godiya ga ra’ayin jama’a da kuma masu yi musu fatan alkhairi a auran nan nasu mai zuwa, a wannan mataki suna so jama’a sub a shawarar su muhimmanci na son kasancewar shi a matsayin sirri.

“Za’a saki sahihan hotunan a lokacin da ya dace.”

A halin yanzu, katin gayyatar auren yay i yawo a kafofin watsa labarai. Kale shi a kasa.

Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga wasu hotunan auran Zahra
Iyalan Buhari sun nesanta kansu daga wasu hotunan auran Zahra

Asali: Legit.ng

Online view pixel