Kudin satan Abacha : Najeriya zata biya kwamishon $79 million

Kudin satan Abacha : Najeriya zata biya kwamishon $79 million

- Gwamnatin Najeirya zata biya kwamishin $79 million kafin kasar Swizalan ta dawo da kudin satan Abacha $400 million

- Dan fafutukan yaki da rashawa, Olanrewaju Suraj, yace irin wannan kwamisho abun kunya ne

- Kafin yanzu, Najeriya ta biya $100 miliyan a matsayin kwamisho ga gwamnatin Swizalan

Kudin satan Abacha : Najeriya zata biya kwamishon $79 million
Kudin satan Abacha : Najeriya zata biya kwamishon $79 million

Da alamun cewa Najeriya fa sai ta biya kudi $79 million ga gwamnatin Swizalan a matsayin fansan kudinta da Abacha ya sace ya kai kasar lokacin shugabancinsa.

Yayinda ake Magana a taron zagayowar ranan yaki da rashwa a Abuja, shugaban kungiyar fafutuka na yaki da rashawa Olanrewaju Suraj yace gwamnatin tarayya zata iya biyan kudi $79 million (N25.2 billion) a matsayin fansan kudin satan Abacha.

KU KARANTA: Timi Frank ya gargadi Saraki

Suraj yace: “Wannan kwamisho na daga cikin yarjejeniyar da kasashen 2 sukayi domin gaggauta dawo da kudaden $400 million (N128billion) da aka kai kasansu ajiya. Kana kuma gwamnatin Najeriya ta amince da sadaukar da $79miliyan a cikin yarjejeniyar.”

Ya kara da cewa: “Wannan abun kunya ne ga gwamnatin Najeriya ta yarda gwamnatin Swizalan ta amsa wannan kwamisho. Ai kamata yayi ma su biya Najeriya kudin ruwa.”

Suraj yace: “Abun kunya, gwamnatinmu na zuwa kasashe tana rook a dawo mata da kudadenta a maimakon bada umurni $321m da gwamnatin Swizalan ta dawo da shi ,daga baya na gano cewa ashe $400m ne. Yarjejeniya ne akayi suka cire na sau ya rage $321m.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel