Dalilin da yasa aure na baiyi karko ba – Yar wasa Chika Ike

Dalilin da yasa aure na baiyi karko ba – Yar wasa Chika Ike

Shararriyar yar wasan Nollywood kuma yar kasuwa, Chika Ike, ta yi bayani kan rashin karkon aurenta.

A wata hira tare da jaridar The Nation, da aka tambayeta ko shin aure a kuriciya na da nasaba da yanda auren yak are a shekaru uku da suka wuce, tace:

Dalilin da yasa aure na baiyi karko ba – Yar wasa Chika Ike
Chika Ike

“Ina ganin akwai dalilai da dama; daya daga ciki na iya kasancewa kuruciya. Wasu mutane na aure da kuruciya kuma auransu na karko. Amma dai yaro yaro ne.

“Akwai abubuwan da baka taba fuskanta ba. Tana iya yiwuwa ka kasa hakuri a inda ya kamata kayi hakuri, ka fahimci abunda ya kamata ka fahimta ko kuma ka bar abunda ya kamata ka bari.

KU KARANTA KUMA: Wata mata yar kasar Kenya mai shekaru 52 ta yi wa mijinta mai shekara 56 duka har lahira cikin dare

“Ina ganin yana da alaka da shekaru da kuma wasu abubuwa da dama a hade kuma da rashin gaskiya a aure. Kowa na da iyaka. Akwai abubuwa da dama a cikin aure da bazaka iya jurewa ba. Iyakar wasu ba lallai ya zamo iyakata ba; iyakata shine daga inda wasu suka fara.”

Kan jita-jitan cewa tana shirin kara shiga hanya kuma, tace:

“Aure makaranta ce mai kyau. Bazan taba guje ma aure ba saboda abune da nake duba zuwa gare shi. Abunda ko wace mace ke buri ne. ko da dai na mayar da hankali kan aikina a yanzu, ina da wani mutun na musamman a rayuwata.”

Abu yayi kyau!

Asali: Legit.ng

Online view pixel