Dubun masu garkuwa da mutane ta cika a Katsina

Dubun masu garkuwa da mutane ta cika a Katsina

'Yansanda sun yi nasarar kubutar da wata babbar manajar hukumar katin dan kasa reshen jihar Katsina, Zuwaira Hamid Bage, kamar yadda jaridar Daily Trust ta buga a shafinta.

Dubun masu garkuwa da mutane ta cika a Katsina
Dubun masu garkuwa da mutane ta cika a Katsina

Wasu karatan maza uku ne suka yi awan gaba da Zuraiwa a tsakiyar dare da misalin karfe daya na dare a Unguwar jerin gudajen Makera Housing Estage dake cikin birnin Katsina.

Wani na kusa da matar ya shaidawa majiyar tamu cewa barayin sun sace Zuwairar ne a cikin gidanta a sa'ilin da mijinta Sanusi Buhari ya fita aikin dare da yake yi a karkashin hukumar kiyaye hadura FRSC a cikin garin Daura.

Ya kara da bayyana cewa ta fice daga motar barayin ne a lokacin da motar take tafiya a hankali daidai kusa da inda 'Yansanda ke binciken ababwen hawa a kan Hanyar Dankama ta karamar hukumar Kaita.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel