Wani Sarki ya rasu a hadarin mota

Wani Sarki ya rasu a hadarin mota

– Sarkin Ijio na Kasar Oyo ya samu rasuwa ta hanyar hadarin mota

– Mai martaba Amunijio na Ijio ya afkawa wata Gingimari ne yayin da yake tuki

– Kwanan ne dai aka kai Sarki Okunade Adegoke kara Kotu

Wani Sarki ya rasu a hadarin mota
Wani Sarki ya rasu a hadarin mota

Mai Girma Sarkin Ijio ya rasa ran sa bayan da ya hadu da wani hadarin mota. Sarkin yana tafiya ne inda zai koma Fadar sa cikin dare. Sarki Okunade Adegoke ya kasance shi kadai ne a cikin motar sa yana tuki yayin da wannan abu ya faru.

Mai Martaba yayi karo da wata gingimari ne a Ranar Larabar nan cikin dare, kimanin karfe 10:00. Ko da mutane suka kawo dauki, an samu Sarkin ya cika. Wadanda suka ga abin, sun ce Sarkin ya aukawa wannan katuwar gingimari ne yayin da yake kokarin kaucewa wata motar.

KU KARANTA: Matar Shugaba Buhari tace ba ta karbar tukwuici

Kwanan nan ne dai aka kai karar Sarkin Kotu, inda ake kukan yana yi wa Talakawa kwacen gonaki da gidaje. An zargi Sarkin da karya kasuwancin Jama’a da dama ta hanyar turo ‘yan ta’adda su karya mutum.

A watan Jiya ne kuma Gwamnatin Jihar Edo karkashin Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ta tsige wani daga cikin masu Sarautar Kasar, An tunbuke Sarki Anselm Eidenojie. Mai Girma Anselm Eidenojie shi yake rike da Kasar Uromi da ke Yankin Arewacin Esan na Jihar Edo. Ana zargin mai martaba da yi wa wata mata shegen duka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel