Hukumar sojin Najeriya ta karawa yaron Obasanjo, Kukasheka girma

Hukumar sojin Najeriya ta karawa yaron Obasanjo, Kukasheka girma

- An karawa jamián soji 225 girma wanda ya kunshi yaron Obasanjo ,Sani Usman Kukasheka da sauran su

- An kara ma yaron Obasanjo da wasu 112 zuwa matsayin Kanal

Hukumar sojin Najeriya ta karawa yaron Obasanjo,Kukasheka girma
Hukumar sojin Najeriya ta karawa yaron Obasanjo,Kukasheka girma

Majalisar sojin Najeiriya ta tabbatar da karawa jami’an soji 227 matsayi a gidan soja.

Jaridar Premiuim Times ta bada rahoton cewa Daga cikin wadanda aka karawa girman sune taron tsohon shugaban kasa Adebayo Obasanjo da kakakin hukumar soji kasa ,Sani Usman Kukasheka.

Karin bayani cikin wasikar wanda aka fitar a ranan 9 ga watan disamba ya nuna cewa Karin girman ya fara ne daga 2014 ga wasu kuma disamba 2016 ga wasu.

An kara musu girma ne bias ga biyayya ga kundin tsarin mulkin soja.

Chukwunedum Abraham,kwamandan Army 2nd Division a Ibadan,tare da wasu 20 an kara musu girma zuwa matsayin Manjo-Janar.

An karama mutane 93 girma zuwa matsayin Birgediya-Janar ,wanda kakakin hukumar ,Sani Usman na ciki. Yaron Obasanjo kuma da wasu 112 an kara musu girma daga matsayin Laftanan Kanal zuwa matsayin Kanal. An kara ma yaron Obasanjo girma ne bayan ya jinkita wajen artabu da yan Boko harm misalin shekaru 2 baya yanzu a jihar Adamawa.

Ku biyomu shafin Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel