Tsoro a jihar Rivers kamar yadda an fara zaben majalisar dokoki a yau Asabar, ku karanta tarihin rikicin zaben jihar

Tsoro a jihar Rivers kamar yadda an fara zaben majalisar dokoki a yau Asabar, ku karanta tarihin rikicin zaben jihar

- Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sun sanya wando daya saboda zaben yan majalisa da za’a yi a yau, Asabar, 10 ga watan Disamba

- Mutanen jihar Rivers zasu zabi wane yan takara suke so tsakanin yan takarar jam’iyyar mai mulki da yan takarar jam’iyyar adawa

- Gwamnan jihar Rivers mai suna Barista Nyesom Wike, dan Jam'iyyar PDP baya so tsohon gwamna da kuma ministan sufuru mai suna Rotimi Amaechi, dan Jam'iyyar APC

Tsoro a jihar Rivers kamar yadda an fara zaben majalisa a yau Asabar
Tsoro a jihar Rivers kamar yadda an fara zaben majalisa a yau Asabar

Jihar Rivers itace jihar na farko a kasar Najeriya da ana yi magudin zabe da yawa da rikici da kuma gwagwarmaya tsakanin jam'iyyu tun an fara gwamnatin demokradiyya a shekarar 1999.

KU KARANTA: Sa’idawa! An gayyaci Gwamna El-Rufai sa ido a zaben kasar Ghana

Zabe a jihar Rivers kamar sojoji da yan ta'addan sun shiga fagen daga ne.

Tun kasar Najeriya ta koma mulkin siyasa bayan gwamnatin soja, jam'iyyar PDP ta jagoranta harkokin jihar Rivers. Amma, a yanzu jam'iyyar APC tana yi yunkurin ta lashe zaben jihar. Dalilin da ya sa jam'iyyar APC tana fuskanta kalubale a zaben jihar, shi ke nan domin yawan mutanen jihar basu so jam'iyyar APC kwata-kwata.

Hukumar zabe ta kasa watau Independent National Electoral Commission (INEC) tana jin tsoro domin yan daba da masu yin magudin zabe suna da yawa a jihar Rivers. A zaben Bara, an kashe mutane sama da 100 a jihar Rivers kadai, yayinda dubun mutane sun ji rauni.

Ku kalli bidiyo wani dan Arewa mai ba shawara ga Shugaban kasa

Za'a yi zaben a yankuna uku da mazabun tarayya guda takwas, sune Akuku-Toru/Asari Toru; Degema/Bonny; Okrika/Ogu-Bolo; Etche/Omuma; Ikwere/Emohua; Khana Gokana; Eleme/Tai/Oyigbo da Opobo/Nkoro/Andoni.

Kuma za'a yi zabe a mazabun jihar, sune Eleme, Gokana, Asari-Toru I, Asari-Toru II, Andoni, Khana II, Etche II, Ikwere, Bonny da Degema.

Asali: Legit.ng

Online view pixel