Sabowar dokar kwastam na cigaba da fuskantar adawa

Sabowar dokar kwastam na cigaba da fuskantar adawa

- Hukumar Kwastam ta Najeriya tace daga ‘daya ga watan Janairun shekara mai zuwa zata hana shigowa da motoci ta kan iyakokin kasar, sai dai a rika shigowa da su ta tashoshin jiragen ruwan Najeriya

- Wata sanarwa da hukumar Kwastam ta fitar da hannun kakakinta Mr. Wale Adeniyi, itace ta bayyana cewa za a fara shigo da motoci ta tashoshin jiragen ruwan Najeriya, wanda zai karawa Najeriya kudaden shiga da take samu daga ketare

Sabowar dokar kwastam na cigaba da fuskantar adawa
All cars must now come in through sea ports

Sanarwar dai ta rawaito cewa shugaban hukumar kwastam kanal Hamid Ali mai Murabus, na cewa matakin umarni ne daga fadar gwamnatin tarayyar Najeriya.

KU KARANTA: Zaka iya sake turo bukatar ciwo bashin ka - Sanatoci zuwa ga Buhari

Ambasada Muktar Gashas, daya daga cikin shugabannin kungiyar masu shigo da motoci ta Najeirya, yace wannan wani yunkurine na ganin an dawo da harkokin sayar da motoci a kasar. Amma wanne irin shiri gwamnati tayi na dawo da harkar gida? Ya kuma kara da cewa dole sai gwamnati ta gano dalilan da suka sa masu shigo da motoci suka daina shigowa ta Lagos suka koma Kwatano.

A daya bangaren kuwa masu daga cikin dillalan motocin hawa a Najeriya, sun bayyana matakin da cewa abin yabawa ne, to sai dai kuma a maimakon wannan mataki kamata yayi gwamnati ta rage kudaden fito da ta ke karba daga hannun masu shigo da motoci, al’amarin da zai sa a dawo da shigo da motoci da sauran kayayyaki ta Najeriya ba wai sai an gabatar da wannan doka ba.

Bayan matakin da gwamnatin Mohammadu Buhari ta dauka na hana shigo da motoci ta kan iyakokin Najeriya dai, a can baya gwamnatin ta dauki wasu makamantan wannan doka akan hana shigo da shinkafa, abin da ya sanya tsadar shinkafar yanzu haka a Najeriya.

Wannan mataki da gwamnatin Najeriya ta dauka zai kara kudaden shiga gwamnatin jahar Lagos amma banda arewa, bayan ita kanta gwamnatin Najeriya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel