Yan shi'a sun sha alwashin maka Kaduna kotu

Yan shi'a sun sha alwashin maka Kaduna kotu

- Kungiyar 'yan uwa Musulmi wato 'yan Shia da ke Najeriya sun ce za su kai karar gwamnatin jihar Kaduna saboda haramta ayyukanta da ta yi

- Kakakin kungiyar Malam Ibrahim Musa ya shaida wa majiyar mu cewa matakin da gwamnatin jihar ta Kaduna ta dauka bai yi musu adalci ba don haka za su je kotu ne domin ta bi musu hakkinsu

Yan shi'a sun sha alwashin maka Kaduna kotu
IMN protesters on Wednesday, August 24

Ya kara da cewa gwamnati ta dauki matakin ne domin bata musu suna a idanun al'uma.

KU KARANTA: Dalilin da yasa muke boyewa jama'a bayan mun lashe zabe - Kakakin Majalissar Jihar Katsina

Gwamnatin jihar ta Kaduna dai ta amince da wasu shawarwari na wani kwamitin bincike da ta kafa bayan tashin hankalin da aka yi tsakanin sojoji da mabiya kungiyar a birnin Zaria a watan Disambar da ya wuce.

Tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar daruruwan 'yan kungiyar ta 'yan uwa Musulmi, a cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International.

Kazalika an kama shugaban kungiyar Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa da 'yan kungiyar da dama, kuma har yanzu ana ci gaba da tsare shi duk da izinin da kotu ta bayar na sakinsa.

A wani labarin kuma, Wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun mamaye Babban kotun tarayya da ke Abuja inda suka gudanar da zanga zangar nuna kin jinin kungiyar Shi'a tare da nuna rashin Jin dadi kan hukuncin kotun wadda ta nemi a saki Shugaban Kungiyar, Malam Ibrahim El Zakzaky.

Masu zanga zangar wadanda ke dauke da kwalaye da ke dauke da sakonni na neman tsige Alkalin da ya zartar da hukuncin Sakin El Zakzaky. Masu tarzoman sun nuna cewa Sakin El Zakzaky zai jefa jami'an tsaron kasar nan cikin hadari kuma zai halatta ayyukan ta'addanci a kasa.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel