Amarya ta rasu a ranar aurenta sakamakon hatsarin jirgi

Amarya ta rasu a ranar aurenta sakamakon hatsarin jirgi

Kusan dukkanin ma’aurata, musamman sabbin aure na samun farin ciki mara misaltuwa a ranar bikin aurensu, sai dai an samu haka a ranar auren Udirley Narques da amaryarsa Rosemere do Nascimento Silva.

Amarya ta rasu a ranar aurenta sakamakon hatsarin jirgi
Ango Udirley Narques da Amarya Rosemere do Nascimento Silva

Yayin da ango da sauran bakin da suka halarci auren da yawansu ya kai mutane 300 suke jiran amarya a wajen biki, a can unguwar Sao Laurenco da Serra, garin San Paulo, Brazil ita kuwa tana nan tana kokarin aikata musu ba zata, inda ta shirya halartan wajen bikin a jirgin sama mai tashin angulu.

Amarya ta rasu a ranar aurenta sakamakon hatsarin jirgi
Amarya kafin shiga jirgi

KU KARANTA:An kama wani mutum da laifin shaƙe budurwarsa har Lahira

Sai dai tashin wannan jirgi ke da wuya, abinka da karfen nasara, sai ya rikito, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar Amarya Rosemere do Nascimento Silva, kanin amarya, mai daukan hoto a bikin auren wanda ke dauke da ciki wata 6, da direban jirgin duk suka rasa rayukansu.

Amarya ta rasu a ranar aurenta sakamakon hatsarin jirgi
Amarya ta rasu a ranar aurenta sakamakon hatsarin jirgi

Yayin da aka kawo ma Ango Udirley Damasceno labarin mutuwar amaryarsa, sai ya kidime. Shugaban shirya taron Carlos Eduardo Batista ya bayyana ma jaridar Sun cewa “duk wani farin ciki da annushuwar da muke da shi a ranar ya bace bayan mun samu labarin mutuwar amarya”

Asali: Legit.ng

Online view pixel