An kama mai siyar ma Fulani makamai a Enugu

An kama mai siyar ma Fulani makamai a Enugu

Jami’an hukumar yansanda reshen jihar Enugu sun kama wani mutum mai suna Alhaji Samaila Garba wanda ake zargi da sana’ar siyar ma yan Fulani makamai.

An kama mai siyar ma Fulani makamai a Enugu

Idan za’a iya tunawa, a yan kwanakin bayan dai ana yawan samun hare haren yan Fulani makiyaya a kauyukan jihar Enugu da dama.

Jaridar Punch ta ruwaito Kaakakin rundunar yansaandan jihar Mista Ebere Amaraizu yana fadin sun fara kama wani dan Fulani mai suna Ibrahim Adamu da bindiga nau’in AK-47 a unguwar Udi na garin Enugu a ranar 29 ga watan Agusta. Bayan ya sha matsa ne, sai Ibrahim ya bayyana sunan Garba a matsayin wanda kawo musu makamai.

KU KARANTA: Ɗan Ƙwallo ya yanke jiki ya mutu yayin da ake tsakar wasa

Tun bayan da Ibrahim ya fallasa Adamu ne yansanda ke ta kokarin bin diddigin neman inda Garba yake, don su kama shi. Amma hakan bai yiwu ba, sai a ranar Talata 6 ga watan Disamba a tashar mota.

Amaraizu yace: “Jami’an Rundunar yansandan jihar Enugu sun samu nasarar kama kasurgumin mai safarar makamai a ranar Talata 6 ga watan Disamba. An samu nasarar kama shi ne bayan, mun samu bayanai daga bakin Ibrahim Adamu da muka fara kamawa dauke da bindiga AK-47.

“An kama mai laifin wanda ya bada sunan shi Alhaji Samaila Garba, mai inkiya Bakassi, bayan Ibrahim ya bayyana mana cewar shi yake siyar musu da makamai. Jim kadan bayan samun labarin kama Ibrahim, sai Garba ya tsere.

“Dubun Garba ya cika a yau Talata yayin da jami’an mu suka samu wasu bayanan sirri da suka bayyana cewar Garba na cikin wata tashar mota, inda a can muka samu nasarar kama shi.”

Kaakakin rundunar yace zuwa yanzu dai mai laifin yana basu hadin kai, tare da basu bayanai masu amfani.

Wanda aka fara kamawa Ibrahim Adamu yace shi dan asalin jihar Nasarawa ne, kuma an kama shi ne dauke da makamin AK-47 da harsasai da dama a dajin Affa. Ya bayyana ma hukumar yansanda cewa ya kasance kiwon shanunsa a yankin Udi, amma yana zama a unguwar Hausawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel