Francisca Odega tayi da na sanin yima kungiyar Najeriya

Francisca Odega tayi da na sanin yima kungiyar Najeriya

Wadda aka haifa a Washington kasar Amurka Francisca Odega kamar tana yin da na sanin ta kama kasar Najeriya ta kasa da shekaru 20 wasa.

Kamar yadda Odega ta bayyana , da ma ace ta zabi doka ma wata kasa wasa ba Najeriya ba saboda rashin goyon bayan kwallon mata a kasar nan, African football. Com suka ruwaito haka.

Francisca Odega tayi da na sanin yima kungiyar Najeriya

Odega wadda tayi nasarar lashe kofi na 3. a kasar Cameroon a hutun makon da ya gabata, inda ta wakilci kasar Najeriya a wasar kasa da shekara 17, da 20 tace ko ohon da ake nunawa ga mata shine abunda tafi da na sani a kai.

Wadda aka haifa a Amurka tace da ace ban yi ma Najeriya kwallo ba da naje nayi ma wata kasar.

Tace yan wasan na kasa da shekara 17 da 2o da ake ta korafi kan rashin kwazon su a gasar kwallon duniya, ya samu asali ne kan rashin shirin da suka yi akan lokaci.

In kuma hakan ta cigaba kasar zata zama tarihi gurin kwallo a nahiyar Afrika.

A halin dai yanzu yan matan wadan da suka wakilci kasar nan a gasar Africa ta mata suna Abuja da karbar kudin sallama daga hannun NFF wato hukumar kwallon kafa ta kasa bayan doke kasar Cameroon da suka yi a wasar karshe da ci 1-0 inda suka lashe kofi.

Ku biyo mu a shafin mu na tuita @naijcomhausa. 

Asali: Legit.ng

Online view pixel