Hukumar Kwastam tayi babban kamu

Hukumar Kwastam tayi babban kamu

Jami’an hukumar kwastam dake tashar jirgin ruwa na Tin-Can Island jihar Legas sun yi carafken cafke wata katuwar sunduki mai tsawon takun-kafa 20 dake makare da shinkafa dafa duka, miyan agushi da sauran kayan abinci irin na Najeriya.

Hukumar Kwastam tayi babban kamu
Kwantrol Bashir Yusuf dauke da kayan abincin

Shugaban Kwastam reshen Tin Can Island Bashar Yusuf ne ya bayyana yadda suka kama katoton sundukin dake dauke da shinkafa dafa duka, miyan kubewa, miyan agushi, faten doya da sauran kayayyakin abinci da aka shigo da shi daga kasar India.

Yayin da kwantrola Yusuf ke Jawabi daidai lokacin dayake mika sundukin ga hukumar kula da tsaftar kayan abinci da maguna (NAFDAC) yace wannan babban laifi ne, musamman a yanzu da gwamnati ta bada daman shigo da na’urorin sarrafa kayan abinci ba tare da biya musu haraji ba.

KU KARANTA: Yarinyar da aka yi ma fyade sau 43,000 (Hotuna)

“Don me wani zai shigo da kayan abincin da ake samun su a Najeriya, musamman yadda ake neman masu zuba hannun jari su zo su bude kamfanuwa?” Inji Yusuf.

Hukumar Kwastam tayi babban kamu
Kwantrola yana mika ma hukumar NAFDAC kayayyakin

Kwantrola Bashir Yusuf yace ofishinsa ya tara ma gwamnati sama da naira biliyan 25.7 a watan Nuwamba kadai, ma’ana an samu kari akan biliyan 25.3 da aka tara a watan Oktoba. Yusuf yace sunyi kokarin tara wadannan makudan kudade ne duk da karayar tattalin arziki tare da karancin shigo da kaya Najeriya.

Yusuf ya cigaba da fadin zasu cigaba da samar da sahihan hanyoyin samar ma kasa kudaden shiga, daga karshe Yusuf ya shawarci masu zuba hannun jari dasu yi kokarin cin gajiyar saukin shigo da kaya Najeriya don samun alhaeri mai yawa.

Shinkafa dafa-duka kuma? Wani abu sai dan Najeriya!

zaku iya samun labaran mu a Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel