Hau! Uwa ta jefar da Jaririyarta a bola
Wata Jaririya tayi sa’ar gaske yayin da wasu dattijan ma’aurata suka tsince ta bayan mahaifiyarta ta jefar da ita a bola.

Dattijan ma’auratan da suka tsinci jaririyar sune Jimmy Alvarez da uwargidarsa Annette Alvarez, sun ci karo da Jaririyar ne yayin da suke yawon ci bola, wato suna yin aikin baban bola inda suke neman gwangwanaye don sabuntasu a kamfani, a cikin haka ne suka tarar da jariryar an lullube tad a tawul.

KU KARANTA:Abin sha’awa: Soyayya irin ta dauri
Dattijo Jimmy Alvarez ne ya dauko jaririyar, amma da fari sai ta kasa motsi saboda tsananin sanyi, amma daya fara shafa mata jiki, nan da nan sai ta fara kuka. Daga nan sai suka kai kara ga hukuma.

Mamaki ya cika Dattijan ma’auratan bayan da hukuma ta gano asalin mahaifiyar jaririyar, ita dai mahaifiyar karamar yarinya ce mai shekaru 13 da tayi cikin shege.
Tuni an mika jaririyar hannun hukuma don samun kulawa a gidan yara, sai dai Dattijan ma’auratan sun bukaci a basu jaririyar su rike, har ma sun sanya mata suna Milagro.

Oh! Allah yasa mufi karfin zuciyanmu
Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng