Labaran da suka girgiza Najeriya a Jiya

Labaran da suka girgiza Najeriya a Jiya

Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman labaran da suka girgiza Najeriya a jiya Litinin, 5 ga watan Disamba.

1. Tashin hankali: Akalla mutane 512 sun kamu da kanjamau a sansanin yan gudun hijra a Borno

Labaran da suka girgiza Najeriya a Jiya

Malam Barkindo Saidu,yace an gano mutane 512 masu cutar kwayar kanjamau a sansunan yan gudun hijra a jihar borno.

2. An kula da annobar ambaliya a shekarar 2016 sosai - NEMA

Labaran da suka girgiza Najeriya a Jiya

Hukumar NEMA tace an samu nasara wajen kula da ambaliyar ruwan sama duk da cewa ruwan sama  a yanzu yafi wanda aka samu a shekaraer 2012.

3. Oyegun zai gana da Saraki,Sanatocin APC akan rikicin APC

Labaran da suka girgiza Najeriya a Jiya

Shugabancin jamíyyar All Progressives Congress (APC) zata gana da shugabancin majalisar dattawa a yau litinin 5 ga watan Disamba ,a sakatariyan jamíyyar a Abuja.

4. Fasto ya mutu yayinda yake Baftizma ga mambobi

Labaran da suka girgiza Najeriya a Jiya

Wani faston kasar Afrika ta kudu ya rasa rayuwarsa bayan ya nutse a Rafin Ulmazi yayinda yake Baftizma kwanakin nan.

5. Abin kunya: Wata budurwa taci duka a shagon gyaran gashi, karanta dalili

Wata budurwa taci na jaki a wani shagon gyaran gashi dake kasar Zimbabwe bayan saurayinta da yayi alkawarin biyan kudin gyaran gashin ya tsere ya barta

6. Shugaban kasa Laberiya ta kawo ma Buhari Ziyara

Labaran da suka girgiza Najeriya a Jiya

Shugaban kasar Laberiya Mrs Sirleaf ta kawo ma shugaba Muhammadu Buhari ziyara fadarsa a Aso Rock Abuja a jiya, 5 ga watan Disamba 2016

Ku biyomu shafin Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel