Wata yarinya da ta kammala digiri da daraja ta farko

Wata yarinya da ta kammala digiri da daraja ta farko

Meye amfanin kyau ba kwakwalwa? Matashiyar ta ba yan mata shawara cewa su bada himma ga karatu, kamar yadda suke bada himma gurin yin kwalliya.

Yanda ma'aikatun kwalliya suke habbaka a kasar nan ta Najeriya, ba abun mamaki bane Kaji kowacce mace tana dukan gaba cewa ita kwararriya ce a bangaren kwalliya, ko kuma kwararriya ce a gurin yin dinki da ado, amma kuma tana da himma a fannin karatu da yawa, duk da cewa suna ta yin fadi tashi na rayuwa.

Wata yarinya da ta kammala digiri da daraja ta farko

Precious Uchechi Okoro ba dadewa ta sa mahaifanta alfahari ba wai gamawa da daraja ta farko ba kawai, a'a ta kasance dalibar da tafi kowa a sashen Agric na makarantar 2016.

Wata yarinya da ta kammala digiri da daraja ta farko

Yarinyar da ta kammala digiri a jami'ar FUTO (Federal University Of Technology Owerri) a bangaren noma (Agric) ta yi amfani da shafin ta na Instagram dan ba da shawara ga yan uwanta mata inda tace" mafarki na da na fara a 2011 ya zamo gaskiya, a shekara ta 2011 da na shiga na kudurta ma raina cewa zan kasance cikin wadanda zasu fito da sakamako mai kyau, da iyawar ubangiji sai gashi mafarki na ya zamo gaskiya, inda yau na fito da daraja ta farko ta digiri, kuma ba nan ba kadai nice dalibar da tafi kowa zama zakara a bangaren mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel