An sanya gidan Beckham a kasuwa, farashi N9bn

An sanya gidan Beckham a kasuwa, farashi N9bn

Fitaccen tsohon dan wasan kwallo kafa David Beckham ya sanya kasaitaccen gidansa na kasar murka a kasuwa, wanda aka mai kudi Naira biliyan tara da miliyan dari shida (N9.6b).

An sanya gidan Beckham a kasuwa, farashi N9bn
Beckham da Victoria

Jaridar Sun ta ruwaito cewar Beckham da matarsa sun yanke shawarar siyar da gidan ne saboda a cewar su yayi musu karami.

Duk da girman gidan, wanda ya kai kusan fadin eka 1 da rabi, baya da dakuna bahaya 9 da suke gidan, akwai kwamin wanka, amma Beckham da Uwargidarsa sun ce suna bukatan gidan da yafi wannan girma saboda yaransu su samu filin wasan kwallo.

An sanya gidan Beckham a kasuwa, farashi N9bn

 

KU KARANTA:Gwamnan jihar Osun ya kaddamar da makaranutun zamani

Rahotanni sun bayyana cewar tun kimanin sama da shekara guda kenan ma’auratan suka sanya gidan a kasuwa, gidan da suka siya akan pam miliyan 14.2 a shekarar 2007, a iya cewa suna bukatan a biya su ninkin kudin da suka siya gidan kenan.

An sanya gidan Beckham a kasuwa, farashi N9bn

Wata majiya ta bayyana cewar Beckham na bukatar gidan dake dauke da filin kwallo, ta yadda yaransu Brooklyn, Romeo da Cruz zasu samu daman buga wasan kwallo yadda suke so.

An sanya gidan Beckham a kasuwa, farashi N9bn

Majiyar ta kara bayyana cewar “Beckham da matarsa Victoria sun nuna damuwa dangane da girman filin wasan gidan nasu, inda suka koka kan yadda yaransu basu da isashshen wajen wasa, ta yadda har sai sun fita makwabta gidajen abokansu suke yin wasa.”

An sanya gidan Beckham a kasuwa, farashi N9bn

Wani kasaitaccen dan kasuwa Stephen Shapiro dake harkar gidaje ya tabbtar mana cewar ya fara samo masu bukatar siyan gidan, yace “a gaskiya gida ne mai kyau, kuma ya dade a kasuwa, na tuna lokacin da suka sa shi a kasuwa, sun mai kudi kusan dala miliyan 30, kimanin pan miliyan 24 kenan.”

Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel