Messi ya baiwa ýaýan Barack Obama babban kyauta

Messi ya baiwa ýaýan Barack Obama babban kyauta

Shahararren dan wasan kwallon kafa dake wasa a kungiyar Basalona Lionel Messi ya aika ma ýayan shugaban kasar Amurka rigunan kwallonsa.

Messi ya baiwa ýaýan Barack Obama babban kyauta
obama

Lionel Messi ya aika ma yayan Obama, Sasha da Malia rigunan kwallonsa na kasar Ajantina wadanda suke dauke da lamba 10 a jikinsu tare da sa hannun dan wasan.

KU KARANTA: Ba zan binciki Mimiko ba-Akeredolu

a yayin wata ziyara da shugaba Obama ya kai tare da iyalansa zuwa kasar Ajantina ya bayyana ma al’ummar kasar cewa yayan nasa suna matukar kaunar Lionel Messi, don haka suke goyon bayan kungiyar Basalona, kuma suna bukatar ganawa da shi.

Messi ya baiwa ýaýan Barack Obama babban kyauta

Duk da cewa dai Messi yana kasar Ajantina domin fafatawa a wasan shiga gasar cin kofin duniya, amma dai bai samu ganawa dasu ba. Sakamakon haka ne dan wasan ya aika musu da rigunan sa dauke da sunayensu, Sasha da Malia.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel