A Kasar Egypt za a fara kama masu yi wa mata kaciya

A Kasar Egypt za a fara kama masu yi wa mata kaciya

- Kasar Masar za ta dauki mataki mai tsanani ga masu yi wa ‘ya ‘ya mata kaciya

- Za a daure duk wanda aka kama na shekaru 15 kamar yadda  Majalisa ta amince

- Za a rika lura da kowane Asibiti ganin an hana kaciya ta mata

A Kasar Egypt, yanzu an kafa doka mai tsanani ga duk wanda aka kama yayi wa diya mace kaciya. Sabuwar dokar da aka sanya kwanan nan za ta sa a daure mutum na shekaru da dama a gidan kaso idan aka kama sa da laifi.

Kasar Egypt din dai tayi garambawul ga dokokin Kasar inda yanzu za a iya jefa mutum yari na shekaru 15 idan har aka kama sa da laifin yi wa yara mata kaciya. A Ranar Talata da ta wuce ne dai Majalisar Kasar ta saka hannu kan wannan doka.

KU KARANTA: Yar shekara goma ta haihu

Ma’aikatar Lafiya ta bada sanarwar cewa daga yanzu, Gwamnati za ta rika bibiyar duk Asibitocin Kasar ganin an kawo karshen kaciya da ake yi wa mata watau abin da ake kira FGM. Ko a baya dai an taba kame wani Likita bayan da yayi wa wata yarinya kaciya.

An saba yi wa mata kaciya musamman a Kasashe irin su Masar, wasu na ganin dai hakan yana da illa ga ‘ya mace.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

 

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel