Najeriya ta gaza sayen Jiragen yaki daga Turai

Najeriya ta gaza sayen Jiragen yaki daga Turai

- Ganin wahalar da ake ta fama da ita wajen sayen jiragen yaki daga Turai, Najeriya ta sauya sheka

- Najeriya na neman jiragen yaki wajen Kasar China da kuma Sojojin Najeriya na ta fafatawa da ‘yan Boko Haram

Najeriya ta gaza sayen Jiragen yaki daga Turai

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wajen ganin an kawo karshen Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda a Kasar, Najeriya na jiran jiragen yaki daga Kasar China da ma Pakistan. Najeriya ta komawa Kasar China da sauran su ne dai bayan sayan kayan yakin daga Turai ya gagara.

Shugaban Hafsun Sojin sama na Kasar, Air Marshall Abubakar Saddique ya bayyana hakan ne ga taron Editan Jaridu a wani taron karin kummalo da aka yi a Birnin Tarayya a karshen wannan makon.

KU KARANTA: '

Shugaban Hafsun Sojin sama na Kasar yace Najeriya na samun taimako daga sauran Kasashen duniya irin su Pakistan da sauran su. Air Marshall Abubakar Saddique yace akwai siyasa kwarai wajen harkar sayan makamai a duniya.

Shugaban Hafsun Sojin na sama ya bayyana cewa kwanan Shugaban Sojojin Pakistan zai zo Najeriya, inda za a tattauna. Haka nan kuma yace Najeriya na jiran wasu kayan yaki daga Kasar da ma China.

 A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

 

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel