Ricikin siyasar Shehu Sani da Elrufa'I na kara kamari

Ricikin siyasar Shehu Sani da Elrufa'I na kara kamari

- Rikicin siyasa tsakanin gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i da dan majalisar dattijai mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani na ci gaba da ruruwa.

- A wani rubutu da yayi a shafinsa na Facebook, Sanata Shehu Sani ya ce wasu, wadanda ya banyana a matsayin 'yan baranda dauke da makamai sun kai hari wani ofishin mazabarshi a tsakiyar Kaduna, inda suka tsarwatsa magoya bayansa dake wani taro, tare da lalata ofishin.

Ricikin siyasar Shehu Sani da Elrufa'I na kara kamari
Senator Shehu Sani ya shawarci buhari kan kudin da Abacha ya sace

Sanata Shehu Sani ya yi zargin cewa, ya na da bayanai dake nuna cewa wasu 'yan siyasa da gwamnan Nasiru Elrufa'i ya ba mukamai ne suka dauki hayar 'yan barandan.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jihar nan tayi wani muhimmin zama kan luwadi

Dan majalisar ya kuma ce a wasu kwanaki da suka gabata, wasu matasa da ya ce an dauki hayar su ne, sun yi yunkurin kona gidan iyayen shi da ke Tudun Wada Kaduna, amma mazauna unguwar suka dakile yunkurin na su.

A bayanan na shi a Facebook, Sanata Shehu Sani ya ce idan wani abu ya same shi, ko iyalanshi, ko kuma magoya bayan shi, ba kowa ne zai dora alhakin akai ba, sai gwamnan jihar Malam Nasiru Elrufa'i

Sai dai a wata sanarwa, mai bai wa gwamnan jihar Kaduna shawara kan sha'anin siyasa, Alhaji Uba Sani ya yi kashedi ga Sanata Shehu Sani da ya dai na wasan yara, ya nuna ya girma.

Alhaji Uba Sani ya ce kamata ya yi Sanata Shehu Sani, wanda yanzu haka jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da shi, ya dai na dora wa gwamnati laifin abin da ya kira tabarbarewar da ta same shi.

Ya ce Sanata Shehu Sani ya shafe watanni goma sha takwas ya na caccakar gwamna da duk manufofinsa, amma gwamnatin jihar ba ta tanka mu shi ba.

Acewar Uba Sani, babu abin da ya shafi gwamnatin jihar da dakatar da Sanatan da jam'iyyar APC ta yi, ya na mai cewa jam'iyyar ce ta ga ya dace ta dauki matakin ladabtar wa akan shi.

A cikin makon da ya gabata ne jam'iyyar APC a jihar Kaduna ta dakatar da Sanata Shehu Sani kan abin da ta ce laifuffukan da ya yi mata.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel