An samu matsaloli a shirin N-Power a jihohin arewa

An samu matsaloli a shirin N-Power a jihohin arewa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara daukan matasa aiki kamar yadda ta yi alkawali, amma yunkurin ya samu cikas a jihohi da dama a shiyar Arewa mussamman a Jihar Neja da Borno da Adamawa da Katsina da Kano da Kebi da kuma jihar Zamfara.

An samu matsaloli a shirin N-Power a jihohin arewa
The N-Power scheme is one of the biggest employment schemes in Nigeria

A watan jiya ne gwamnatin tarayya ta fitar da jerin sunayen matasa dubu 200 a shirin na N-Power, wanda tace sun sami nasarar shiga kashin farko na shirin da gwamnati tayi don tallafawa matasa marasa aikin yi.

KU KARANTA: Shirin N-Power: Namu ba irin na su bane inji fadar shugaban kasa

Sai dai shirin ya gamu da korafe korafe a yawancin jahohin Arewa musamman a jahar Borno inda da rikicin Boko Haram ya dai dai ta. Sanata Baba Kaka Bashir Garbai, mai wakiltar Borno ta tsakiya a Majalisar Dattawa, yace an kware su a jahar Borno domin ana amfani da yanar gizo ne wajen yin rijistar masu neman aikin. Sai dai jihar Borno na fama da matsalolin hanyoyin sadarwa da wutar lantarki.

A bangaren Majalisar wakilai Mohammed Tahir Mongono, daga jahar Borno yace mutum biyu kadai aka dauka daga karamar hukumar da yake wakilta, sai dai yace sun dauki mataki kasancewar sune wakilan mutane inda suka kai kuka ga hukumar dake kula da wannan shiri.

A cikin matasa dubu 200 an dauki dubu 150 a matsayin malaman makaranta, dubu 30 kuma zasu yi aiki a fannin Noma a shirin na N-Power. Yayin da ragowar dubu 20 zasu yi aiki a fannin Kiwon lafiya.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel