An kori wasu malamai saboda laifin lalata da mata

An kori wasu malamai saboda laifin lalata da mata

- Gwamnatin tarayya ta sallami wasu malaman kwalejin kimiyya da fasaha ta Auchi da ke jihar Edo bisa samun da laifin yin fasikanci da dalibai mata da zimmar kara masu maki a jarrabawa

- Haka ma, gwamnati ta rage girma ga wasu malaman kwalejin su 16 bisa laifin da ya jibinci fasikanci da dalibai mata

An kori wasu malamai saboda laifin lalata da mata
Kaduna Polytechnic

Wannan mataki na gwamnati ya biyo bayan wani bincike ne da aka gudanar sakamakon wani rahoto da ya fallasa yadda dalibai maza ke tura 'yan matansu su kwana da malamai don su samun damar cin jarrabawa.

A wani labari makamancin wannan kuma, Kungiyoyin Kare hakkokin mata a Najeriya sun bukaci gwamnatin kasar ta gaggauta daukar matakan hana aurar da mata da wuri bayan kasar ta amince da shirin kungiyar kasashen Afirka na yaki da auran wuri.

KU KARANTA: Ana dab da samun riga-kafin cutar kanjamau

Wannan ya biyo bayan kaddamar da shiri na musamman da gwamnatin kasar ta yi domin kare hakkokin mata da kuma aiwatar da dokar da za ta hukunta masu tilasta musu auran.

Gwamnatin Najeriya ta amince da dokar hana aurar da mata da wuri a shekarar 2003, amma ya zuwa yanzu Jihohi 23 kawai suka aiwatar da dokar.

Hukumar UNICEF ta ce akalla ‘yan mata 4 daga cikin 10 ake aurar da su kafin su kai shekaru 18 a Najeriya.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel