N-power ya sha ban-ban da na sauran

N-power ya sha ban-ban da na sauran

- Mai taimakawa mataimakin shugaban Najeriya, ofishin da ke kula da alhakin shirin samawa matasa aiki na N-Power, Hafiz Ibrahim, ya ce matasa dubu 200 da aka dauka aiki ba za su fuskanci matsalar albashi ba

- A ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba din nan ne dai ake sa ran shirin na N-Power zai fara aiki

N-power ya sha ban-ban da na sauran
N-Power

Hafiz ya bayyana hakan ne a hirarsa da majiyar mu, a inda ya ce shirin na N-Power, ba zai zama kamar sauran ayyukan gwamnati ba da ake daukar ma'aikata ba tare da albashi ba har na tsawon watanni.

Ya ce matasan da aka dauka za su dauki albashi a watan farko na fara aikinsu wato Disamba.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya zata sake tankade wasu yan N-Power

Ya kuma kara da cewa gwamnati ta rigaya ta kebe kudade a kasafin kudin kasar wadanda da su ne za a biya matasan.

Sai dai kuma wasu matasan da suka samu aikin na N-Power wadanda kuma suka zanta da majiyar mu, sun ce duk da cewa yau ne ake fara shirin amma su kam ba su san inda za su je ba domin fara aiki.

To amma Hafiz Ibrahim ya ce, ranar farko ta fara wannan shiri za ta zama lokacin sake tantance matasan domin gane unguwowinsu da garuruwansu, kafin daga bisani a fada musu wurin da za su je aiki.

A watan jiya ne dai gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin sunayen matasa dubu 200 da ta ce sun samu nasarar shiga kashin farko na shirin na N-Power.

Matasa dubu 150 ne aka dauka a matsayin malaman makaranta.

Dubu 30 kuma za su yi aiki a fannin noma, yayin da ragowar dubu 20 din za su yi aiki a fannin kiwon lafiya.

Miliyoyin matasa ne dai a kasar ke fama da rashin aikin yi.

Kuma 'yan kasar sun zura ido domin ganin yadda gwamnatin Muhammadu Buhari za ta shawo kan wannan matsala.

Magance matsalar aikin yi dai na daya daga cikin batutuwan da shugaba Buharin ya yi alkawarin magancewa lokacin yakin neman zabensa.

Kididdiga ta nuna cewa akwai kimanin matasa miliyan 70 daga cikin mutanen Najeriya miliyan 167.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel