Nigeria ce ta biyu a cutar kanjamau a duniya

Nigeria ce ta biyu a cutar kanjamau a duniya

- Wani tsohon jami'in Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da hada yaduwar cutar kanjamau ko kuma HIV/AIDS, a Uganda, Musa Ahmed Bungudu, ya ce Najeriya ce ta biyu a cutar a fadin duniya

- Tsohon jami'in ya ce kasar Afirka ta Kudu ce ta farko a yawan mutanen da ke dauke da kwayar cutar ta kanjamau

Nigeria ce ta biyu a cutar kanjamau a duniya
Health workers checking for malaria and HIV from some of the attendees

Alhaji Bungudu ya kara da cewa a Najeriyar an haifi jarirai kimanin dubu 60 masu dauke da kwayar cutar.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Borno ya karyata Buhari?

Ya kuma ce rashin mayar da hankali wajen dakile cutar ne ya janyo wa Najeriyar halin da take ciki.

Dangane kuma da nasarorin kan yakar cutar, Bungudu ya ce, wasu kasashen na Afirka sun yi samu nasara amma fa banda Najeriya.

Akwai dai kimanin mutane miliyan 37 da ke dauke da wannan cuta a fadin duniya.

Ranar 1 ga watan Disambar kowace shekara, ta kasance ranar yaki da cutar mai karya garkuwar jiki watau kanjamau, ta duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ce dai ta ware ranar da manufar wayar da kan al'umma a kan illolin da ke tattare da cutar, da kuma hanyoyin da za abi wajen hana yaduwarta da ma rashin kamuwa da ita.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel