Wata budurwa ta caccaki Adaeze Yobo

Wata budurwa ta caccaki Adaeze Yobo

Abun mamaki ne da ban dariya yadda wasu mata suke magana akan iyalin wasu mutane, musamman yan uwan su mata.

Wata budurwa ta caccaki Adaeze Yobo

Mata dan kwallon Najeriya kuma tsohuwar sarauniyar kyau wato Adaeze Yobo.

A kwanakin baya ne dai a kafafan yanar gizo aka caccaki matar dan kwallon kafar Najeriya wato Adaeze Yobo a shafin Instagram, inda daya daga cikin mata mabiyan shafin nata ta caccaketa dayin ciki duk shekara.

Bayan labarin daya fita cewar Adaeze din da mijin nata wato Josep Yobo suna saran samun yaron su na uku nan bada dadewa ba a shafukan sadarwa da kuma zumunta, sai kawai wata yarinya taje shafin nata na instagram ta caccake ta. Inda ta rubuta cewar ' kin kara yin ciki kuma, kaichonki, kada ki mantafa kefa matar aure ce.

KU KARANTA: Muhimman batutuwan ranan lantana

Matar dan wasan dai dake saran haihuwan nan da nan ta maida mata da martani, inda tace mata; @finearmy meye matsalar haihuwa na na uku, alokacin da nake cika shekara 7 dayin aure? Kina nuna damuwar ki tare da kuma mamaki a shafin naki akan hakan ma.

Ta bayyana kina nuna matukar damuwar ki ma, akan abin da bai dame kiba. Zan ci gaba da haihuwa da sunan yesu, babu wani abunda zai faru sai dai alheri. Domin hakan shike nuna cewar inada lafiya kuma ina cikin lokaci na.

Abin mamaki....wasu mutane basu da kunya fa.

Ku biyomu a shafinmu na tuwita: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel