Dahiru Bauchi ya yi kira da a tausayawa talaka

Dahiru Bauchi ya yi kira da a tausayawa talaka

Matsalar tsadar rayuwa a Najeriya ke ci ma talakawa tuwo a kwarya saboda haka ne shugabanni na addini da na al'umma ke kiran gwamnatin kasar da ta sauya salo ko talaka zai samu dan sassauci.

Dahiru Bauchi ya yi kira da a tausayawa talaka
Sheikh Dahiru Usman Bauchi and Alhaji Aminu Masari, Katsina  state governor

Bayan sun kammala taronsu na darikar Tijjaniya da suka gudanar a Yola babban birnin jihar Adamawa, Shaikh Dahiru Bauchi, daya daga cikin shugabannin addinin musulunci a Najeriya yana ganin dole ne gwamnatin tarayya ta tashi tsaye ta magance matsalar kuncin rayuwa da ake fama da ita a kasar yanzu.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jihar nan tayi wani muhimmin zama kan luwadi

Shaikh Dahiru Bauchi yace a ji tausayin mutane saboda suna cikin wahala musamman wahalar abinci. Yace a tausaya masu a samu hanyar da za'a tare abincin da aka noma cikin gida domin kada a yi waje dashi. Wanda ma yake waje a shigo dashi a kara kan na gida.

Malamin ya ci gaba da cewa a dubi duk abubuwan da suka dami mutane a yi masu maganinsu kama daga gwamnatin tarayya zuwa na jihohi da na kananan hukumomi. A tausayawa jama'a.

Yayinda ya juwa kan takunsakan da ake samu da 'yan kungiyar Shi'a da hukumomin kasar, Shaikh Bauchi yace akwai abun dubawa. A hada kai tsakanin musulmai da makwaftansu da ba musulmai ba domin a zauna lafiya. Kowa yayi abun dake gabansa tunda kasar ta ba kowa damar yayi addinin da yake so. Yace to kowa yayi nasa kada a tsangwameshi, shi kuma kada ya tsangwami kowa.

Yace kodayake tashin hankali a arewa maso gabas yayi sauki amma ta wajen Zamfara sai karuwa yake yi. Suna rokon Allah ya kawo sauki.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel