Ya tsinci dimbin gwala-gwalai a gidan daya gada

Ya tsinci dimbin gwala-gwalai a gidan daya gada

Mutuwar wani tashin wani, da wannan ne wani mutum ya tsinci dami a kaala, bayan rasuwar wani dan uwarsa.

Ya tsinci dimbin gwala-gwalai a gidan daya gada
kudi

Wannan mutum dan kasar Faransa ya tsinci damin Zinari da suka kai nauyin kilo 100 da aka boye su a cikin wani gida daya gada, bayan rasuwar dan uwansa. Mutum ya tsinci gwala gwalan ne makare cikin gidan, inda ya tsinci wasu a karkashin kayayyakin sawa, cikin akwati, cikin bayi, karkashin kujeru har ma da cikin kwalaban giya.

KU KARANTA:An damfari Obasanjo daruruwan miliyoyi

Ya tsinci dimbin gwala-gwalai a gidan daya gada
gidaje

Jimillan yawan gwala gwalan sun kai guda 5000, a cewar rahoton. Asali ma mutumin na cikin yin kwaleman sabon gidan nasa daya gada ne yayin daya tsinci gwala gwalan. Takardun shaida sun nuna cewar tun a shekarar 1950 aka siya gwala gwalan, tuni dai mutumin ya siyar da dukiyar. Ko kun ga laifinsa? Idna kai ne ya zaka yi?

Idan kai ma kana bukatar nemo naka dukiyar, toh Allah ya bada sa’a.

Zaku iya samun labaran mu a shaifn Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel