Shugaban kasa Buhari na shirin soke auren yar sa da dan biloniya? (bidiyo)

Shugaban kasa Buhari na shirin soke auren yar sa da dan biloniya? (bidiyo)

Bayan kai jakunkunan lefe na kamfanin LV da surukan Zahra Buhari, Ahlin Indimi suka kai kwanan nan, labarai sun nuna cewa mahaifinta shugaban kasa Muhammadu Buhari bai ji dadin yanda dukkan bayanan ya kai kafofin watsa labarai ba.

Shugaban kasa Buhari na shirin soke auren yar sa da dan biloniya? (bidiyo)
Shugaban kasa Buhari, da yar sa Zahra Buhari

Daily Correspondents authoritatively sun ruwaito cewa: “an dakatar da bikin auran Zahra, yar shugaban kasar Najeriya Buhari gad an shahararen dan kasuwan nan, Mohammed Indimi, wanda aka shirya yi a ranar 4 ga watan Disamba na 2016. Daily Correspondents sun kawo cewa, an dakatar da bikin ne sakamakon umurnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda bisa ga majiyar dake kusanci da ahlin gidan biyu, hankalinsa bai kwanta da ido da aka sanya wa auren yar tasa ba a kafofin zumunta, musamman a labaran jakunkunan lefe da aka kawo wa Zahra da farashin say a kai N44m.

Anyi bikin sanya rana a tsakanin gidajen biyu a Aso Villa, Abuja a ranar Juma’a, 18 ga watan Nuwamba, amma an sanya ranar bikin tsakanin ranar Laraba 30 Nuwamber da kuma Lahadi 4 ga watan Disamba, 2016, ya kamata ace anyi bikin cikin sauki kamar yadda shugaban kasa ya bukaci auran ya kasance a sawwake, kuma wadanda zasu halarci taron su kasance makusanta da abokai. Amma ido da kafofin watsa labarai suka sanya ya canja komai yanzu kuma shugaban kasa bai ji dadi ba.

KU KARANTA KUMA: Buhari, da matarsa sunyi bikin zagayowar haihuwar jikarsu

Shugaban kasa Buhari na shirin soke auren yar sa da dan biloniya? (bidiyo)
Ahmed Indimi da Zahra Buhari

Bayan haka, an kuma tattaro cewa shugaban kasa wanda ya bada umarnin cewa jami’an tsaro su binciki Ahmed da inda yake samun tarin dukiyarsu, hankalinsa bai kwanta da mahaifin angon ba, Alhaji Mohammed Indimi saboda kusancin sa da tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Badamosi Babangida, IBB. Tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida ya kasance ubangidan biloniya Mohammed Indimi, kuma tsohon shugaban kasar bai so Buhari ya tsaya takara a 2015 ba.

A halin yanzu dai babu mamaki shugaban kasa Buhari ya bada daman a ci gaba da shirin biki nan gaba.

Kalli bidiyo a kasa:

Hmm! muna nan muna sanya ido

Asali: Legit.ng

Online view pixel