Rikicin APC:Buhari yayi bayani alakarshi da Tinubu

Rikicin APC:Buhari yayi bayani alakarshi da Tinubu

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayani akan alakarshi da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin na kut-da-kut

- Yayi kira ga mambobin jamíyyar da su dainan jita-jitan da zai kawo rabuwan kai a jamíyyar

- Shugaban kasa ya yabi Tinubu da karfin halinsa da kokari

Rikicin APC:Buhari yayi bayani alakarshi da Tinubu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar way an Najeriya cewa akwai kyakkyawan alaka tsakaninsa da Tinubu sabanin abinda mutane suke rayawa.

Ya bayyana hakan ne ta mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, inda ya bayyana cewa rahotannin bogin a ake bayar wa kawai domin cin mutuncin Tinubu ne.

KU KARANTA: Wani mutum ya kera mota mai tafiya a ruwa da kan hanya

Shehu yace shugaban kasa Buhari ya fusata akan zantukan cewa shi da Tinubu sun zama makiya kuma akwai cecekuce tsakaninsu.

Shugaban yayi faric cikin maganar Tinubu na cewa ba zai yaudari jamíyyar a zaben Ondo ba kuma ya cika alkawarinsa.

Ya siffanta Tinubu a matsayin dan siyasa mai kima da mutunci a idon duniya kuma ba zaá taba manta gudunmuwar da ya bada wajen nasarar jamíyyar ba.

Mai Magana da yawun shugaban kasan ya baiwa mutane shawaran cewa su daina yada jita-jitan da zai kawo rigima tsakanin shugaba Buhari da Tinubu kuma shi Buhari na alfahari da Tinubu da kuma matsayinsa a jamíyyar.

Kana shugaba Buhari ya yabawa Tinubu akan mika sakn taya murnan da yayi ma Akeredolu akan nasarar sa a zaben jihar Ondo.

Buhari yayi kiira da mambobin jamíyyar da yi watsi da wasu maganganun da zai raba kan mutane kuma su sani cewa gwamnatin shugaban na mayar da kanta wajen shugabanci ne.

A biyomu a shafin Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel