Yan gudun hijira dake a Borno na bukatar agaji

Yan gudun hijira dake a Borno na bukatar agaji

- Kungiyoyi da dama na ci gaba da yunkurin tallafa wa 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu, a Najeriya

- Duk da irin nasarorin da dakarun kasar da na makwabtan kasashe suka samu na kwace yawancin garuruwa da 'ya'yan kungiyar Boko Haram suke rike da su a baya, har yanzu, mafiya yawan wadanda abin ya shafa na zaune ne a sansanoni daban-daban da hukumomi suka kafa

Yan gudun hijira dake a Borno na bukatar agaji
Security officers make sure women are orderly in a queue at an IDP camp in the Northeast. Photo credit: Reuters

A yanzu haka kuma 'yan gudun hijrar na ci gaba da kokawa kan halin kuncin da suke ciki.

KU KARANTA: Dangote zai gina kamfanin casar shinkafa a Kano

A karshen mako ne dai wata tawagar kungiyar matan sojijin sama na Najeriya, ta kai ziyara ga 'yan gudun hijira da ke sansanin garin Bama a jihar Borno.

Ziyarar ta kunshi kai tallafin kayan abinci da na bukatun yau da kullum ga 'yan gudun hijirar. Kimanin mutane dubu goma sha uku ne dai ke zaune a sansanin 'yan gudun hijirar na Bama.

Majiyar mu da ta kasance tare da tawagar ta rawaito cewa yara kanana da mata da tsafoffi ke ta sowa da murna a lokacin da tawagar ta isa da kayan tallafin. Wata babbar matsala da 'yan gudun hijirar ke fama da ita baya ga ta abinci, ita ce rashin isasshen makewayi.

Har wa yau, akwai jama'ar da ke kwana a sararin Allah ko dan tantin da ake kafawa ba su samu ba. Fatan mutanen dai shi ne zaman lafiya da kwanciyar hankali su dore a Nigeria, a kuma kawo karshen tada kayar baya ta kungiyar Boko Haram.

Hakan ne dai zai ba su damar komawa gidajensu, domin gaba da rayuwa kamar yadda aka saba a baya.

Tun a watan Maris din shekarar 2015 ne dakarun Nigeria suka yi ikrarin fatattakar mayakan Boko Haram daga garin na Bama.

Sai dai har yanzu jama'ar da suka yi gudun hijira ba su samu damar komawa gidajen su ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel