Buhari aikinka na kyau - Rabaran Mbaka

Buhari aikinka na kyau - Rabaran Mbaka

- Rabaran Mbaka ya yaba salon yaki da cin hanki da rashawa na shugaba Buhari, ya kuma ce shubagan ya ci gaba da wannan yaki da ya samo a bangaren shari’a

- Limamin cocin darikar Katolika wanda ya saba janyo ka-ce-na-ce a ya ce wannan yakin da Buhari ya ke yi daga Allah ne

Buhari aikinka na kyau - Rabaran Mbaka
Buhari da Rabaran Mbaka a yayin wata ziyara

Shugaban mujami’ar cocin Adoration ta darikar Katolika da ke Emene a jihar Enugu, Rabaran Fada Ejike Mbaka ya jinjinawa gwamnati mai ci yanzu a kokarin da ta ke yi na tsaftace al’amuran kasar nan.

Rabaran Mbaka ya ce, Allah ne ya kawo juyin-juya hali a kasarnan ta hanyar amfami da shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban mujami’ar wanda ke magana kan samun wasu alkalai da hannu damu-damu a badakalar cin hanci da rashawa, ya ce , ci gaba da da kame alkalan wani abin cigaba ne mai faranta rai.

Rabaran Fada ya yi wadannan kalamai ne a lokacin gudanar da wani taron addu’oi don bikin shiga sabuwar shekarar shari’o’I ta shekarar 2016 da 2017 na jihar Enugu wanda ka aka gudanar a wurin ibadar cocin a Emene.

Sannan ya kuma kara da cewa, wasu alkalan zargi ne kawai ake yi musu, amma binciken da ake yi a kansu na da kyau domin idan har aka same su da laifi, a aikasu gidan yari, domin hakan ya zama darasi ga sauran.

A cewar jaridar Vanguard, Mbaka  ya bayyana kame alkalan da cewa: “Kame alkalan  wani sabon sauyi ne daga mai duka domin gobara ce daga kogi, wanda sai ya taba dukkannin bangarori 3 na gwamnati.

“Idan juyin-juya hali ya kankama , babu wanda ya san iya inda zai tsaya sai mai duka.

“Don haka ina mai kira ga alkalai da su tsaya ga gaskiya ko kuma su shiga hannu, kuma duk wanda ya kama su, dole ne a yaba masa.”  

Ku biyo mu a shafin Tuwuita a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel