Wani tababbe ya kashe uwar sa

Wani tababbe ya kashe uwar sa

Wani wanda kan sa ba dadi ya kashe mahaifiyar sa har lahira

- Wannan tabbabe dai ya kammala karatun san a Jami’a

- Hakan ya faru ne a garin Otukpo na Jihar Benue

Wani tababbe ya kashe uwar sa
Wani tababbe ya kashe uwar sa

 

 

 

 

 

 

Wani abin Allah-kyauta ya faru a Unguwar Ufia da ke Garin Otukpo a Jihar Benue inda aka samu wani sabon tababbe ya kashe mahaifiyar sa. Jaridar Daily Post ce dai ta rahoto yadda abin ya faru.

Godwin Orinya wanda yayi karatu a Jami’ar Jos ya kama uwar sa da duka har sai da ta mutu. Godwin dai sabon tababbe ne, dan kuma asalin Garin Ado na Jihar ta Benue. Bayan Godwin ya kashe uwar ta sa, ya kama hanya ya tsere abin sa.

KU KARANTA: PDP na ganin uwar-bari

Wani tababbe ya kashe uwar sa

 

 

 

 

 

Kwamishinan Yan Sanda na Jihar

Kwanan nan ne dai kan wannan bawan Allah ya fara zama ba dadi, don haka aka wuce da shi wajen wani mai magani a Garin Agboke. A nan wajen mai maganin ne ya kama mahaifiyar ta sa da duka har ya ga bayan ta.

Shugaban’yan Sanda na Yankin ya tabbatarwa Jaridar Daily Post faruwar wannan abu, ya kuma bayyana cewa har yanzu ana neman wannan tababbe ruwa a jallo, domin gudun a kara maimata irin na jiya.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel