Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 30 a wata karanbatta

Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 30 a wata karanbatta

Kimanin Sojoji 6 ne suka samu raunuka daban daban a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba yayin wata karanbatta da suka yi da yayan kungiyar ta’addanci Boko Haram a kan titin Maiduguri zuwa Bama, jihar Borno, inji rahoton Premium Times.

Rahoton ya kara bayyana cewra sama da yayan kungiyar ta Boko Haram 20 aka hallaka yayin gumurzun.

Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 30 a wata karanbatta

An ruwaito cewa yan Boko Haram sunyi ma Sojoji shigan bagtatan ne, wato ba zato ba tsammani yayin da suke raka jerin gwanon motocin jami’an karamar hukumar Gwoza. Ana tsakar tafiya kawai sai gungun yayan Boko Haram su 40 suka bude ma ayarin motocin wuta.

Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 30 a wata karanbatta

KU KARANTA:El-Rufai da Shehu Sani: Ana tuhumar gwamna da cin hanci

Shugaban karamar hukumar Gwoza, Sa’eed Sambo ya tabbatar da faruwar lamarin, amma yace Sojojin dake tare dasu sun nuna jarumta inda suka mayar da wuta, suka kashe mutum 20. Sambo yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe, inda ya kara da cewa “yan ta’addan sun fara wurgo mana bom kafin su fara yi mana ruwan harsashi.”

Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 30 a wata karanbatta

Daga karshe rahoton ya ruwaito wani babban jami’in Soji wanda shima ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace an garzaya da Sojojin da suka jikkata zuwa asibitin Sojoji dake Barikin Maimalari.

zaku iya samun labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel