Gwamnatin Kaduna ta bayyana su waye masu satar mutane

Gwamnatin Kaduna ta bayyana su waye masu satar mutane

- Sace mutane ana garkuwa dasu a Najeriya tamkar ya zama ruwan dare gama gari saboda babu wani yankin kasar da ba'a sace mutane

- Gwamnan Kaduna ya shaidawa majiyar mu cewa gwamnati ta damu da maganar sace mutane da a keyi a jihar ta damesu amma kuma baya son ya bayyana shirin da su keyi da jami'an tsaro na kawo karshen aika aikar

Gwamnatin Kaduna ta bayyana su waye masu satar mutane
Governor Nasir El-Rufai and other state officials during the flag-off of the programme

Yace gwamnatinsa tana iyakar kokarinta saidai watakila lamarin ya fi karfin jihar saboda haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta shigo ciki.

KU KARANTA: Sabon kundin tsarin mulki zai kammalu a sabuwar shekara

Gwamnan yace kawo karshen wannan bala'in sai gwamnatin tarayya ta fito da wani shirn farma masu satar mutane a duk jihohin kasar lokaci daya. Idan ana yi jiha jiha to da zara an farmasu a waccan jiha zasu zo wannan haka zasu dinga yi har a gaji a barsu.

Gwamnan yace a jihar Kaduna sun kama masu satar mutane fiye da dari hudu kuma yawancinsu, fiye da dari uku Fulani ne 'yan shekaru goma sha takwas zuwa talatin.

Inji gwamnan kullum ya zauna da shugabannin Fulani yana gaya masu su tashi tsaye su shawo kan lamarin domin satan mutane da fashi da makami da sace shanu basa cikin halayen Fulani. Dole ne shugabannin Fulani su tashi su gyara.

A gwamnatance gwamnan yace suna nasu tsare tsaren na yakar wannan bala'i.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel