Chelsea gida na ne- inji Moses

Chelsea gida na ne- inji Moses

- Victor Moses yace doka wasa a Chelsea shine abunda ya fi so                                   

- An yi rohoton cewa kungiyar Barcelona na neman Moses                                            

- Dan wasan Najeriya yana taka leda da kyau a kungiyar Chelsea a kakar wasar bana

Dan wasan Najeriya Victor Moses yace baya da niyyar barin kungiyar Chelsea a halin yanzu, wanda ya wanke ma magoya bayan  kungiyar Chelsea damuwa kan rade-raden cewa ze tafi kungiyar Barcelona.

Sunan Moses ya zama kanun labarun kusan kowacce jarida kan cewar kungiyar Barcelona suna son su saye shi watan Janairu 2017 in an bude kasuwar sayen yan wasa.

Chelsea gida na ne- inji Moses
Victor Moses

Dan shekara 25 yana taka leda da kyau a kasar shi da kungiyar shi ta Chelsea a kakar bana, shi yasa ya bayyana cewa ba nan kusa ze bar kungiyar Chelsea ba.

KU KARANTA: 

Na samu sabon gida, Chelsea gida na ne, zan gode ma kocin mu kan yardar da yayi man kuma ya bani damar taka leda, ina so in cigaba da doka ma Chelsea wasa.

Ina matukar farin cikin doka ma kungiyar Chelsea wasa a gasar kakar bana, ina so in ce Chelsea ya zama gida na.

Victor Moses ya kayatar a wasar da ya doka ranar asabar 26 ga watan Nuwamba da Tottenham inda ya zura kwallo 1 a yayin wasar.

Ku biyo mu a shafin mu na tuita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel