An kara korar Koci Mourinho na Man Utd ana wasa

An kara korar Koci Mourinho na Man Utd ana wasa

- Alkalin wasa ya nuna Koci Jose Mourinho na Man Utd jan kati ana cikin wasa

- Man Utd ta tashi kunnen doki a wasan

- Ba wannan ne karo na farko da aka kori Mourinho daga cikin fili ba

An kara korar Koci Mourinho na Man Utd ana wasa

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wani Alkalin wasa ya kora Koci Jose Mourinho daga cikin fili yayin da ake wani wasa. Alkali Jon Moss ya nunawa Jose Mourinho jan kati yayin da ake karawa a Filin wasan Man Utd na Old Trafford a Jiya, Lahadi.

Alkalin wasa ya ba dan wasa Pogba kati ne bayan yayi lanbo, hakan ta sa Koci Mourinho ya fusata, har yayi kwallo da wani goran ruwa. Ko dai da aka sake haskawa, sai aka ga cewa lallai dan wasan lanbo kurum yayi, ya fadi ba tare da an taba sa ba.

KU KARANTA: An bar baya da kura a zaben Amurka

Ba yau aka saba korar Koci Mourinho daga fili ba, ko a wasan Man Utd da Burnley, an kori wannan Koci. An dai tashi wasan na Jiya 1- 1. A bara ma dai wannan Alkalin ya ba Mourinho jan kati lokacin yana Chelsea.

A baya dai, Hukumar FA ta Ingila ta ci tarar Koci Jose Mourinho. Hukumar da ke kula da kwallon kafa na Ingila tace kalaman Koci Jose Mourinho ga wani Alkalin ta, Anthony Tailor, ba su yi mata kyau ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel