Abubuwa 5 game da Akeredolu

Abubuwa 5 game da Akeredolu

Rotimi Akeredolu dan takarar gwamna a jam’iyyar APC ne ya lashe zaben da aka yi a ranar Asabar 26 ga watan Nuwamba a jihar Ondo bayan da ya doke abokan takararsa daga PDP da APC

Abubuwa 5 game da Akeredolu

Ga wasu abubuwa 5 da ya kamata ka sani game da gwamna mai jiran gado na daga APC

1. Asali

Iyayayen Rotimi Akeredolu malamin coci ne, mahaifinsa shi ne Rabaran J. Ola Akeredolu daga zuriyar Akeredolu, mahaifiyarsa kuwa Grace B Akeredolu mai wa’azain kirista ce ‘yan asalin Ese ta jihar Ondo.

2. Karatu

Gwamna mai jiran gado ya yi karatun a kwalejin Layola ta Ibadan, ya kuma halarci Jami’ar Ife, wacce a yanzu a ke jami’ar Obafemi  Awolowo, a inda ya karanta shari’a a shekarar 1977. Ya kuma zama cikakken lauya a shekarar 1978.

3. Shugabanci

Gwamnan mai jiran gado tsohon shugaban kungiyar Lauyoyi ne a shekarar 2008, an kuma zarge shi da cin hanci da rashawa wannan mukami daga baya aka yi watsi da zargin bayan wani bincike.

KU KARANTA KUMA: APC na murna yayinda Akeredolu zai zama zakara

4. Siyasa

Akeredolu ya shiga harkar siyasa ne shekarar 2012, ya kuma ya taba yin takarar gwamna a karkashin Jam’iyyar ACN, a inda suka kara da gwamna mai barin gado Olusegun Mimiko, da kuma Olusola Oke na jam’iyyar PDP a waccan lokaci.

5. Nasarori:  kungiyar lauyoyi ta kasa NBA ta sawa babban ofishinta da ke Abuja sunansa saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen cin gaban kungiyar. Akeredolu yana rike da matsayin babban lauya na kasar mai lambar SAN wacce ya samu a shekarar 1998, sannan ya kuma taba rike mukamin babban mai gabatar da kara na jihar Ondo daga sherakar 1997 zuwa 1998 .

Tabbasa kowa ya ci zomo, ya ci gudu.

Ku biyomu a shafinmu na Tuwita a @naijcomhusa

&t=2s

Asali: Legit.ng

Online view pixel