APC na kan gaba a zaben Gwamnan Jihar Ondo

APC na kan gaba a zaben Gwamnan Jihar Ondo

- Bayanai da ke zuwa daga kafofi da dama sun nuna cewa APC ke kan gaba a zaben Ondo

- Jam’iyyar PDP mai mulkin Jihar na bi mata a baya da kuma ana ta rikici tsakanin Manyan Jam’iyyu game da zaben na Jihar Ondo

APC na kan gaba a zaben Gwamnan Jihar Ondo

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ana kokarin ganin an zabi Sabon Gwamna a Jihar Ondo wanda zai canji Olusegun Mimiko zuwa shekara mai zuwa. ‘Yan takara fiye da 20 suke harin wannan kujera, sai dai akwai manyan ‘Yan takara guda 3; Rotimi Akeredolu, Eyitayo Jegede da kuma Olusegun Oke.

Jam’iyyar PDP dai ta koka tun farko da shirin zaben, PDP na ta fama da rikici iri-iri na Kotu bayan da a da aka ce Jimoh Ibrahim ne zai rike mata tuta a zaben na Ranar Asabar. Kwamishinan INEC na Jihar, O. Agbaje yace Hukumar INEC ta fa shiryawa wannan zabe.

KU KARANTA: Ana rikici a Jihar Ondo

Yanzu haka dan takarar APC Rotimi Akerodolu ke gaba, yayi wad an takarar PDP, Tayo Jegede nisa, haka nan kuma sun tserewa Olusola Oke na Jam’iyyar AD da aka farfado a Jihar.

Cikin Kananan Hukumomi fiye da goma da aka samu sakamakon su, Akerodolu na APC yana da kuri’a 209322, haka kuma dan takarar PDP yana da kuri’u 200389. Ko wa zai zama Sabon Gwamnan Ondo?

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

 

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel