Ana zaman makokin Fidel Castro a Cuba

Ana zaman makokin Fidel Castro a Cuba

- Tsohon shugaban kasar Cuba Fidel Castro ya bar duniya

- Fidel Castro ya rasu yana da shekaru 90

- Tsohon shugaban ne ya jagoranci juyin juya-halin da aka yi a Kasar Cuba shekaru 50 da suka wuce

Ana zaman makokin Fidel Castro a Cuba

[caption id="attachment_1063107" align="a__left" width="800"] fidel castro[/caption]

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Gidan BBC ta rahoto cewa ana zaman makokin rasuwar Tsohon Shugaba Fidel Castro a Kasar Cuba. Kasar Cuba za tayi zaman makoki na kwanaki har 9 domin jimamin rashin Tsohon Shugaban na ta.

An tashi ne karshen wannan makon da labarin rasuwar Fidel Castro, wanda ya bar duniya yana mai shekaru 90 cif. Kamar yadda BBC ta rahoto, magoya bayan Shugaban sun ce Castro ya bautawa Kasar Cuba.

KU KARANTA: Atiku ya cika 70

Fidel Castro ya karbi mulkin Kasar Cuba tun a shekarun 1950s, sai da ya shafe shekaru fiye kusan 50, kafin dan uwan sa Raul Castro ya karbi mulki a shekarar 2006. Castro ya jagoranci Kasar karkashin Jam’iyyar sa ta kwaminisanci.

Za a kona gawan Castro mako mai zuwa a Birnin Santiago. Danuwan sa kuma Shugaban na Cuba, Raul yace ko ba Fidel, Cuba za tayi nasara. An sha yunkurin kashe Fidel Castro, sai dai da sauran kwana gaba wajen Fidel Castro.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

 

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel