A sakamakon farko na zaben Ondo ta bayan gida ya nuna cewa gwamma mai barin gado Olusegun Mimiko da dan takarar jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede sun kai batansu a mazabansu.

[caption id="attachment_1050041" align="alignnone" width="500"] 'Yan takara a zaben gwamnan jihar Ondo[/caption]
A sakamakon da Legit.ng ta soma tattarawa na zaben gwamna na jihar Ondo da aka gudanar a yau, na nuna cewa gwamna Mimiko da Jegede na PDP sun ci a mazabansu.
Gwamna mai barin gado Mimiko ya ba maras da kunya a mazabarsa mai lamba 7 a akwatin zabe na 2 da ke a karamar hukumar Ondo ta yamma a inda ya kada kuri’arsa.
Dan takarar jam’iyyar PDP Eyitayo Jegede kuwa ya samu kuri’u 184 a da ya kayar da dan takarar jam’iyyar APC Rotimi Akeredolu mai kuri’u 77, da kuma dan takarar jam’iyyar AD Olusola Oke wanda ya samu kuri’u 32.
KU KARANTA KUMA: Na'ura ta hana gwamna zabe a Ondo
A mazabar gwamna Mimiko kuwa, PDP ta samu kuri’u 176, APC kuwa 40, yayin da AD ta samu 15 .
A yawancin rumfunar zabe an gama kada kuri’u, an kuma soma kirga kuri’u a yawancin inda aka kada kuri’un.
A wani labarin kuma, wasu fusatattun masu kada kuri’a da ke kan layin kada kuri’a sun fattaki wani jigon jam’iyyar APC tare da yi masa kememe a kokarinsa na sayen kuri’unsu .
Hakan ta bayyana ne ta hanyar wani hoton bidiyo an inda aka nuna wasu jamu’an tsaro sun kewaye jiigon a yayin da masu zaben suka yi masa kawanya tare da yi masa a ture a bisa zargin kokarin sayen kuri’unsu
Lamarin ya faru ne a rumfar zabe ta St, Thomas da ke Akure babban birnin jihar Ondo, A cewar gidan Talbijin na jihar, watau Ondo TV, wanda aka yiwa aturen jigo ne a jam’iyyar APC, kuma sunansa Tunji Light Ariyo.