APC na Kokarin sayen kuri'a ?

APC na Kokarin sayen kuri'a ?

Wani hoton bidiyo da gidan talbijin na jihar ya dauka ya nuna yadda wani jigo a jam’iyyar APC ke kokarin sayen kuri’un masu zabe a lokacin da suke kan layin kada kuri’arsu a zaben gwamna da ake yi a jihar Ondo  

APC na Kokarin sayen kuri'a ?

[caption id="attachment_1063210" align="alignnone" width="760"] Zaben jihar Ondo[/caption]

Wasu fusatattun masu kada kuri’a da ke kan layin kada kuri’a sun fattaki wani jigon jam’iyyar APC tare da yi masa kememe a kokarinsa na sayen kuri’unsu a zaben gwamnan da ake yi a jihar.

Hakan ta bayyana ne ta hanyar wani hoton bidiyo da aka dauka, aka kuma yada a dandalin sada zumunta da muharawa.

A hoton bidiyon, dai ga jamu’an tsaro na rakiyar jigon a jami’an taron sun kewaye shi a yayin da masu zaben suka yi masa kawanya tare da yi masa a ture a bisa zargin kokarin sayen kuri’u.

KU KARANTA KUMA: An soma zargin Magudi a zaben Ondo

Lamarin ya faru ne a rumfar zabe ta St, Thomas da ke Akure babban birnin jihar Ondo.

A cewar gidan Talbijin na jihar, watau Ondo TV, wanda aka yiwa aturen jigo ne a jam’iyyar APC, kuma sunansa Tunji Light Ariyo.

Babu dai wani karin bayani dangane da faruwar lamarin.

Wanda ake zargi Tunji Ariyo bai ce komai ba, haka ma jam’iyyar APC ko kuma dan takararta Mista Akeredolu.

Ku biyo mu a Tuwita a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel