Sojojin Najeriya sun mamaye Zamfara

Sojojin Najeriya sun mamaye Zamfara

Mazauna wasu yankuna na jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce an samu kwararar dakarun sojin kasar dauke da manyan makamai zuwa cikin jihar.

Mutanen da majiyar mu ta yi hira da su sun ce ba su saba ganin yawan sojojin da aka tura jihar ba.

Sojojin Najeriya sun mamaye Zamfara

Hakan dai na faruwa ne kwanaki kadan bayan masu fashin shanu sun addabi jihar, lamarin da ya kai ga kashe akalla mutum 150.

Barayin shanun sun fi addabar mazauna yankin Dansadau da ke karamar hukumar Maru.

Wani mazaunin yankin, Malam Nuhu Dansadau, ya shaida wa majiyar mu, "Mun ga kananan jiragen yaki uku - da wasu manya da motoci sama da 27 dauke da sojoji. wasu sun tafi yankin da aka kashe masu hakar zinare, wasu kuma sun tsaya a Magami da Dansadau. Mutanen yankin na cike da murna."

KU KARANTA: Ta Leko ta kowa a shirin N-Power

Da ma dai gwamnatin kasar ta sha alwashin murkusshe barayin shanun da suka addabi yankin.

Tun farko dai daman Mutanen da 'yan bindigan suka sace su fiye da araba'in akan hanyarsu ta zuwa kasuwa ranar Juma'ar da ta gabata a yankin Dansadau cikin karamar hukumar Maru sun samu 'yancinsu ne biyo bayan wani sulhu da aka yi.

An samu yin sulhu da 'yanbindigan ne tsakanin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa a karkashin shugabancin mataimakin gwamnan jihar da kuma 'yan bindigan.

To saidai gwamnatin jihar kawo yanzu bata fito fili tayi wani cikakken bayani ba akan sulhun amma rahotanni sun nuna cewar 'yan bindigan sun bukaci a mayar masu da shanunsu da aka kwace kafin su sako mutanen. Bisa ga alamu gwamnati ta cika wannan sharadin na 'yanbindigan.

Yayinda yake gabatar da mutanen ga gwamnan jihar Zamfara mataimakin gwamnan yace ya koyi babban daratsi a jagorancin kwamitin 'yanto mutanen da yayi.

Mataimakin gwamnan ya kira shugabannin sassa, da shugabannin siyasa, da jami'an tsaro cewar idan ana son zaman lafiya da kwanciyar hankali to su nisanci zalunci. Yace abu na biyu da ya koya shi ne ta hanyar tattaunawa ana iya samun zaman lafiya tare da warware duk wata matsala.

Duk da cewa sai da nuna karfi ake shawo kan mazalunta cewa akwai hukuma amma karfi kawai baya kawo zaman lafiya sai an hadashi da lumana da jawo hankali.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel