FG ta siya ma FRSC motocin aiki kirar Najeriya

FG ta siya ma FRSC motocin aiki kirar Najeriya

A ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba Majalisar ƙolin tarayyar Najeriya ta lamunce da a siyan ma hukumar kare haddura ta kasa (FRSC) motocin aiki da kudinsu ya kai Naira miliyan 464.

Dama dai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana da fahimtar cewa ta hanyar siyan kayayyakin da ake sarrafawa a gida Najeriya ne kadai tattalin arzkin ƙasar nan zai haɓɓaka.

FG ta siya ma FRSC motocin aiki kirar Najeriya

Motocin da za’a siya ma FRSC sun haɗa da A-kori-kura guda 50 da za’a siya daga kamfanin Innoson Motors dake garin Nnewi, sai Mota 301 kirar Pijo guda 27 da za’a siya daga kamfanin Peugeot dake Kaduna.

KU KARANTA: Yan daba sun farfasa Ofishin kamfen Jimoh Ibrahim a Ondo

Kamar yadda minista ƙwadago Chris Ngige ya bayyana, yace Gwamnati ta yanke shawarar siyan motocin ne daga kamfanunuwan gida don tabbatar da sabon shirin ta na haɓɓaka tattakin arzikin kasar nan.

“Majalisar ta amince a siya ma FRSC motocin ne don kara mata kwarin gwiwar gudanar da ayyukanta. Majalisar ta amince a siyo motoci kirar A-kori-kura guda 40, da kuma Pijo 301 guda 27. Wannan ya dace da manufar gwamnatin mu a karkashin shugabancin Muhammadu Buhari na tayar da komadar tattalin arzikin kasar nan. jimillar kudaden da za’a kashe wajen siyan motocin ya kai N464m. farashin motocin Innoson ya kai N299m sai na Peugeot N164m” inji Nigige.

A bayan dama kiraye kiraye ya yawaita ga ýan Najeriya dasu dinga siyan kayayyakin da ake sarrafawa a Najeriya don karkatar da tattalin arzikin kasar nan daga dogara da man fetur.

Tun kafin wannan mataki da Gwamnati ta dauka, Sanata Ben Murray Bruce shi ya fara siyan mota daga kamfanin Innoson, wannan ya sanya majalisar dattijai siyan motocin su na aiki daga kamfanin.

Z'a iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel