Atiku ya bikin cika shekaru 70

Atiku ya bikin cika shekaru 70

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 cif-cif a ranar Juma’a 25 ga watan Nuwamba, ya kuma gudanar da wani kwarya-kwaryar biki a gidansa tare da iyalansa

Atiku ya bikin cika shekaru 70

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi bikin cika shekaru 70 da haihuwa, a baya dai Atiku ya bayyana cewa shi ne mutum guda daya tilo a zuruiyarsa da Allah Ya yiwa wannan baiwa na ganain wannan shekaru a raye.

Atiku Abubakar ya yi bikin murnar zagayowar wannan ranar a wani kasaitaccen biki da yayi  tare da iyalansa.

Atiku ya bikin cika shekaru 70
Atiku da iyalansa a yayin bikin[/caption]

[caption id=

Atiku ya bikin cika shekaru 70
Atiku da 'ya 'yansa maza a yayin bikin[/caption]

[caption id=

Cikin wandanda suke aikewa Atiku Abubakar murnar zagayowar wannan rana sun hada da shugaba Muhammadu Buhari da Jagoran APC Bola Ahmed Tinubu da saurana sauran 'yan Najeriya.

Atiku shi ne tsohon mataimakin shugaba Obasanjo a shekarun 8 da yayi yana mulki a karkashin jam'iyyar PDP. Ya kuma bar jam'iyyar da gabannin babban zaben shekarar 2015 a inda koma jam'iyyar  APC ya kuma marawa Muhammadu Buhari baya, bayan da ya sha kaye a zaben fidda gwani na jama'iyyar a inda ya zo na uku.

Gogaggen dan siyasa Atiku Abubakar ya yi fice wajen fagen kafa jam'iyya da kuma tafiyar da tsarin siyasar tafiya da kowa a ba tare da banbancin kabila ko addini ba.

Sai Atiku ba ya rabo da shiga ka-ce-na-ce na siyasa a inda kwanan nan ya suke yi sa toka-sa-katsi da gwamnan jihar Kaduna Ahmed El Rufa'i kan wasu manufofin gwamnati.

An kuma zargin Atiku da hannu wajen haddasa rikici a jam'iyyar PDM inda shugabancin jam'iyyar ya kori shugabanta na tsawon lokaci Bashir Yusuf, wanda a hirarsa da 'yan jaridu Bashir din ke zargin Atiku da kitsa wannan kora domin mayar da jam'iyyar tasa a wani mataki na wukar baya don cimma wani buri na son zuciya a 2019.

Ku biyomu a shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa

 

Asali: Legit.ng

Online view pixel