Sojoji za su kawo karshen masu dana bam

Sojoji za su kawo karshen masu dana bam

– Sojoji sun sha alwashin kawo karshen ta’addanci a Najeriya

Ana ta samun yawan masu yin kunar bakin wake

Rundunar Sojin Kasar nan tace ta gano yadda za a kawo karshen wannan bala’i

Sojoji za su kawo karshen masu dana bam

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Rundunar Sojin Najeriya tace kwanan nan za a kawo karshen masu dana bam a Kasar. Rundunar Sojin Kasar tace ta gano yadda za a kawo karshen wannan lamari na ta’addanci da yayi kamari musamman a Arewa ta Gabas.

Kwamandan Rundunar Operation Lafiya Dole, Manjo-Janar Lucky Irabor yace ba shakka abin ya kusa zama tarihi. Kwamandan yayi wannan maganar ne a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.

KU KARANTA: 'Yan Neja-Delta sun gane kuskuren su

Jaridar The Nation ta rahoto Kwamandan yana mai cewa Soji tayi galaba bisa ‘Yan Boko Haram, kuma ya tabbatar da cewa za a kawo karshen masu kunar bakin wake. Rundunar Operation Lafiya Dole  na dai cigaba da karasa gamawa da ragowan ‘Yan Boko Haram.

Ko a kwanakin baya an rahoto cewa an harbe wani dan Boko Haram har lahira yayin da yake kokarin shiga sansani ‘Yan gudun Hijira watau IDP da ke Maiduguri ya dana bam. Bayan an gane sa, nan take aka shiga baza masa wuta har ya mutu.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa    

 

https://youtu.be/wXmmTEAKDxo

Asali: Legit.ng

Online view pixel