Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Wani dan asalin kasar Kenya mai suna Anthony Buluma Samba yayi ma budurwar sa mai sunaGettie Nthiiri, wani abun abin mamaki, bayan daya nemi auren ta a filin jirgin sama. 

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Gettie tana mamakin neman auren nata.

Ya dai zabi babban  filin jirgin sama na Jomo Kenyatta a matsayin inda zai bayyana ma masoyiyar tasa cewar yana neman auren ta, bayan da yasan cewar Gettie zata dawo Kenyan kuma zata sauka a wannan filin jirgin saman.

KU KARANTA: Yaro ďan shekara 3 ya ceci rayuwar mahaifinsa

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Wannan shine abu na farko alokacin da ta futo daga cikin filin jirgin saman.

Abokan Anthony dai da yan uwan sa da kuma abokan aikin sa sun taka mahimmiyar rawa a wajen inda suka daga kwalaye mai dauke da rubutu na aka rubuta cewar ' Gettie zaki aure ni?'

Gettie wacce ma'aikaciya ce a ma'aikatan mahukuntar kasar Kenya, tagi mamaki tare da kuma kaduwa dangane da ganin wannan al'amarin alokacin data sauka filin jirgin saman.

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Jama'a suna yi masu tafi bayan data yarda da bukatar daya zo mata.

Tadai ga Anthony rike da fulawa a hannun sa inda ya rike zoben alkawari kuma da dayan hannun, sannan kuma ya tsugunna akan gwiwar sa guda daya yana rokon ta data yarda dashi a matsayin mijin ta. A bayan sa kuma abokan sane rike da kwalaye, abun dai daga gani, batasan haka zai faru ba gaba daya.

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Anthony yayi godiya ga Allah bayan da Gettie ta amince da bukatar sa. Sai suka rungume juna, inda nan da nan kuma masu kida da kuma bushe-bushe suka rikita wajen da kide kide da bushe bushe.

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Gettie na cikin tunani tare da mamakin wannan al'amarin. Inda jama'ar dake wajen suka fara tafi da kuma shewa akan al'amarin.

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Masoyan sun rungume junan su, inda masu kida kuma suka fara kida. Anthony dai ya kwashe rana guda yana shirin wannan al'amarin, inda yace "bayi na bane, yin Allah ne faruwan hakan, kuma ina kara gode masa sosai".

Hoton neman auren wani dan kasar Kenya a filin jirgin sama.

Abokan Anthony suna daga kwalaye dake dauke da rubutu iri-iri, wanda ke nuna cewar suna taya abokin sune neman yardar soyayyar Gettie.

Haka kuma Anthony ya godema yan uwansa da abokansa da suka tayashi wannan aikin. Kuma ya kara godema Allah dangane da sa'ar daya samu na yarda da shi da masoyiyar tashi tayi.

Sannan kuma ya kara godema masoyiyar tasa wato Gettie, da yarda dashi datayi, inda yayi mata alkawarin kasancewa tare da ita har abada.

Masoya suna cikin nishadi. Muna tayasu murna.

Ku biyomu a shafinmu na tuwita: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel