‘Yan Boko Haram sun sake kasha wani Laftanan Kanal

 ‘Yan Boko Haram sun sake kasha wani Laftanan Kanal

- Hukumar sojin kasan Najeriya ta tabbatar da mutuwan wani baban kwamandan wanda yan Boko Haram suka kashe

- Da farko bai rasa ransa ba amma ya cika daga baya a asibiti

- Wannan shine laftanan kanal na 3 da zai rasa ransa a cigaba da yaki da yan Boko Haram a watanni 2

 ‘Yan Boko Haram sun sake kasha wani Laftanan Kanal

[caption id="attachment_1049819" align="alignnone" width="300"] Lt. Col B.U. Umar[/caption]

Hukumar sojin kasan Najaeriya ta tabbatar da mutuwan wani baban kwamandan wanda yan boko haram suka kasha bayan ya ji mumunan rauni.

A wata jawabin da suka saki ajiya laraba,23 ga watan nuwamba, Manjo janar Lucky Irabor,kwamandan sojin kasa a yankin arewa maso gabas ya tabbatar da rasuwan BU Umar da kuma wani Laftanan Mukhtar a harin da Boko Haram suka kai.

KU KARANTA:Boko Haram ta kashe karin wasu sojojin 6

“A ranan 15 ga watan Nuwamb misalign karfe 9 na safe , rundunar sojin kasa sun ci karo da wata bam da aka shuka a hanyar Bitta – Pirang daga baya kuma aka bude musu wuta.

“Rundunar sojin sun fitittiki yan boko haram din amma abin talaici Lt Kanal BU Umar ya rasa rayuwarsa. Baya ga haka wani Laftanan Muktar ma ya rasu yayinda soji 8 na jinya a asibiti. Zuwa yanzu dai ana sa ran samun saukinsu.

“A dukka ayyukan da akeyi,an ceto mutane 5,235 daga hannun yan Boko Haram,Yace

Zaku tuna cewa kwanakin baya an yi rashin Lieutenant Colonel Abu Ali tare da wasu soji guda 6 .

A biyo mu a shafinmu na Tuwita: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel