Ana cigaba da muzgunawa musulmai a kasar Myanmar

Ana cigaba da muzgunawa musulmai a kasar Myanmar

Gwamnatin kasar Myanmar ko Burma tana daukan duk matakan hana dimbin Musulman kasar 'yan jinsin Rohingya hanasu ficewa daga kasar yayinda kuma ta cigaba da kutunta masu.

Akwai alamar cewa duk da kiranye-kiranyen da kasashen duniya ke mata, gwamnatin kasar Myanmar (ko Burma) ta daura anniyar ci gaba da aiwatarda kudurinta na toshe hanyoyin fita kasar don hana wa dimbin tarin Musulmi ‘yan jinsin Rohingya ficewa kasar ta jiragen kwale-kwale don gujewa masifar kuntatatawar da ake musu a wannan kasar da aksarin mutanenta duk mabiya addinin Buddha ne.

Ana cigaba da muzgunawa musulmai a kasar Myanmar
Muslims praying at the prayer ground

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta daukewa Dangote biyan haraji

Bayan sun share wattani biyu suna fuskantar samamen da ma’aikatan tsaro ke kaiwa a kansu ne, daruruwan Musulmin Rohingya din suka yi yunkurin karya doka wajen tsallakawa zuwa cikin kasar Bangladesh dake makwaptaka da su.

Ko a cikin makon jiya ma majalisar dinkin duniya ta bada rahoton cewa mutane kamar 300,000, wadanda galibinsu duk Musulmi ne, a ka raba da muhallansu, yayinda kungiyoyin kare hakkokin Bil Adama suka tabattarda cewa an kashe akalla 80 daga cikinsu a lokacinda ma’aikatan tsaron Myanmar din suka abka musu.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel